Mali:'Yan Ta'adda 25 Sun Gudu Daga Gidan Kaso
Hukumomin tsaron kasar Mali sun sanar da tserewar wasu 'yan ta'adda 25 daga gidan kaso na kudancin Bamako babban birnin kasar
Cikin wata sanarwa da suka fitar a jiya Litinin, hukumomin tsaron kasar Mali sun ce wasu 'yan ta'adda 25 dake tsare a wani gidan Yari na kudancin birnin Bamako sun gudu bayan da suka jikkata jami'an tsaron gidan Yarin guda biyu.
Wannan Lamari na zuwa ne yayin da a ranar lahadin da ta gabata, wasu 'yan ta'adda suka halba makamin iguwa zuwa barikin sojan kasar ta Mali a garin Tounbouctou dake arewacin kasar, to saidai babu wani da ya samu rauni sanadiyar harin.
A ranar 14 ga wannan wata na Avrilu da muke ciki, sansanin Dakarun tsaron sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya sun fuskanci hare-hare daga 'yan ta'adda a garin na Tounbouctou.
A cikin shekarun baya-bayan nan rikicin cikin gida da kuma hare-haren 'yan ta'adda da na tsaurin ra'ayi na kara tsananta a kasar ta Mali.