Mali : An Gano Malaman Bogi 10,000
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30238-mali_an_gano_malaman_bogi_10_000
Hukumomi a kasar Mali, na bincike kan gano suwa ke da hannu a badakalar cin bulus da albashin wasu malaman bogi su 10,000 a kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:44+00:00 )
Apr 24, 2018 06:33 UTC
  • Mali : An Gano Malaman Bogi 10,000

Hukumomi a kasar Mali, na bincike kan gano suwa ke da hannu a badakalar cin bulus da albashin wasu malaman bogi su 10,000 a kasar

Binciken dai na shafar malaman makarantu boko na faramari na karkara a cewar wata sanarwar ma'aikatar ilimin kasar.

Sanarwar ta ce daga cikin malaman makarantun 16,000 da ake biya albashi 10,000 na bogi ne.

Ko baya ga malaman da akwai daliban bogi wadanda gwamnati ke ba kudin alawus a karkara.

Gwamnatin kasar ta ce taka kashe sabar kudade da yawansu ya kai Bilyan 41 na Cfa a ko wacce shekara kan harkar ilimi.