Nijar : Ana Bukin Cika Shekaru 23 Na Hadin Kan Kasa
Apr 24, 2018 11:04 UTC
A Jamhuriyar Nijar, yau ne 24 ga watan Afrilu ake gudanar da bukin ranar hadin-kan ‘yan kasa, ranar da ta samo asali daga yarjejeniyar zaman lafiya ta farko da aka kulla tsakanin ‘yan tawaye da gwamnatin kasar a irin wanan ranar ta shekarar 1995.
An dai kulla yarjejeniyar ne a lokacin tsohon shugaban kasar marigayi Janar Ibrahim Ba’are Mainasara.
Wasu kasashen masu makotaka da Nijar din ne da suka hada da Chadi, Mali, Burkina Faso da Aljeriya ne suka shiga tsakani locacin rikicin inda kuma sansanta jituwa tsakanin Azbinawa da ke daukeda makamai da kuma gwamnatin ta Nijar.
Tun dai lokacin ne a zagayowar ranar ta 24 ga watan April ake gudanar da bukukuwa domin kara hada kan al’ummar ‘yan kasar.
Tags