ICC Ta Sake Watsi Da Bukatar Belin Laurent Gbagbo
Apr 24, 2018 11:05 UTC
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta sake yin watsi da bukatar bada belin tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo.
Mista Gbagbo, dai na fuskantar shari'a ne kan zargin cin zarafin bil adama, a yayin rikicin da ya biyo bayan zaben kasar Ivory Coast na 2010.
Shafin kotun ta ICC, ya rawaito cewa, kotun ta yi watsi da bukatar sakin talala ga tsohon shugaban kasar ta Ivory Coast da gagarimin rinjaye.
Su dai lauyoyin dake kare Mista Gbagbo, suna bukatar a yi masa sakin talala, saboda dalilai na rashin lafiya, saidai kotun ta ce Gbagbo, ya na samun cikakiyar kula ta sha'anin kiwan lafiya.
Tun a watan Nowamba na 2011 ne aka tsare da Laurent Gbagbo mai shekaru 73 a La Haye.
Tags