Aljeriya : Sojoji 12 Sun Mutu A Hadarin Jirgi Mai Saukar Ungulu
-
hadarin wani jirgi mai saukar ungulu
Ma'aikatar tsaro kasar Aljeriya ta sanar da mutuwar wasu sojojin kasar 12 da jikkatar wasu biyu sakamakon hadarin wani jirgin sojin kasar mai saukar ungulu.
Jirgin na daukan kaya kirar MI-171 na rundinar sojin saman kasar ya fadi ne sakamakon matsala a daidai lokacin da yake shawagi a yankin Adrar dake kudancin kasar jiya Lahadi.
kamfanin dilancin labarai na kasar APS ya rawaito karamin ministan tsaro kasar kuma babban hafsan sojin kasar Ahmed Gaid Salah na cewa na tabbatar da hakan tare da bada umurnin gudanar da kwararen bincike domin gano musababin faduwar jirgin.
Wannan dai ba shi ne karo farko ba da ake samun haduran jiragen saman soji a kasar Aljeriya ba, inda ko a watan Oktoban 2014 faduwar wani jirgin sojin kasar a kudanci ta hadasa mutuwar wasu sojin kasar biyu, yayin da kuma a watan fabrairu 2014 wani hadarin jirgin saman a gabashin kasar yayi sanadin mutuwar sojojin kasar 77.