Afirka Ta Kudu: Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin Albashi Mafi Karanci
(last modified Thu, 26 Apr 2018 06:37:34 GMT )
Apr 26, 2018 06:37 UTC
  • Afirka Ta Kudu: Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin Albashi Mafi Karanci

Gamayyar kungiyoyin kwadago a kasar Afirka ta kudu na gudanar da gangami da jerin gwano a biranan kasar, domin nuna rashin amincewa da tsarin albashi mafi karanci.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, an gudanar da jerin gwanon ne a birane daban-daban na kasar a jiya Laraba, domin yin watsi da tsarin nan na biyan rand 20 ($1.6) a kowace sa'a guda, a matsayin albashi mafi karanci a kasar.

An amince da wannan tsarin albashi na biyan rand 20 a kowace sa'a guda  a matsayin mafi karancin albashi a  kasar Afirka ta kudu ne tun a cikin watan Nuwamban 2017, kuma ana sa ran za a fara aiki da shi daga ranar 1 ga watan Mayu mai kamawa.