Najeriya : Sojoji Sun Murkushe Harin Boko Haram A Maiduguri
Apr 27, 2018 01:16 UTC
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun murkushe wani hari da mayakan Boko Haram suka yi yunkurin kaiwa birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin kasar a jiya Alhamis.
Kafin hakan dama rahotanni sun mazauna birnin sun yi ta jin karar harbe-harben manyan bindigogi da yammacin jiya, lamarin da ya kai ga wasu mazauna birnin tserewa daga gidajensu.
Wasu rahotanni sun ce mayakan sun yi kokarin kutsawa ne cikin barikin sojin Giwa inda ake tsare da kwamandodin su da dama.
Kawao yanzu dai bayanai sun ce al'amura sun koma kamar yadda aka saba bayan an dakile yunkurin harin.
Tags