Mali : An Cafke Mutane Biyu Dake Da Hannu A Harin Grand-Bassam
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3034-mali_an_cafke_mutane_biyu_dake_da_hannu_a_harin_grand_bassam
Hukumomi a Mali sun sanar da cafke wasu 'yan kasar 2 da ake zargi da hannu a harin da kungiyar Al'Qaida ta dauki alhakin kai a wurin shakatawan nan na Grand-Bassan a kasar Cote d'Ivoire / Ivory Coast.
(last modified 2018-08-22T06:58:02+00:00 )
Mar 28, 2016 00:33 UTC
  • 'yan sanda na bincike a wurin da aka kai hari na Grand Bassam
    'yan sanda na bincike a wurin da aka kai hari na Grand Bassam

Hukumomi a Mali sun sanar da cafke wasu 'yan kasar 2 da ake zargi da hannu a harin da kungiyar Al'Qaida ta dauki alhakin kai a wurin shakatawan nan na Grand-Bassan a kasar Cote d'Ivoire / Ivory Coast.

Da yake karin haske kan hakan laftana-kanal Modibo Nama Traoré na hukumar samar da bayanai a kasar ta Mali ya ce jam'ian tsaro jandarma ne suka cafke mutanen biyu a arewacin kasar.

Wata majiya daga gwamnatin Mali ta ce an cafke mutanen ne daban-daban a ranakun Asabar da Lahadi a biranen Tumbuktu, Goundam da Gossi dake arewacin kasar

Dama kafin hakan hukumomin kasar ta Cote d'Ivoire / Ivory Coast sun sanar da kame mutane 15 da ake zargi da hannu a harin na ranar 13 ga watan nan da ya yi sanadin mutuwar mutane 19.

Saidai a cewar hukumomin har yanzu ana neman wani mutun mai suna Kounta Dallah da ake tuhuma da shirya kai harin da kungiyar Aqmi reshen Al'QAIDA a kasashen larabawa na Magreb ta dauki alhakin kaiwa.