Majalisar Dinkin Duniya Tana Kokarin Warware Rikicin Siyasar Kasar Madagaska.
(last modified Sat, 28 Apr 2018 11:48:11 GMT )
Apr 28, 2018 11:48 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Tana Kokarin Warware Rikicin Siyasar Kasar Madagaska.

Babban sakataren Majalisar dinkin dunya Antonio Gutteres ya bada sanarwan cewa majalisar tana kokarin shiga tsakani don warware sabon rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar Madagaska.

Tashar talabijin ta France 24 ta nakalto babban sakatarin yana fadar cewa tuna ya aike da jakadansa na musamman zuwa kasar ta Madagaskar a matsayin mai shiga tsakani don warware rikicin siyasar kasar wanda ya kai ga tashe-tashen hankulka a cikin kwanakin da suka gabata a kasar. 

Yan adawa a kasar ta Madagaska sun jera kwanaki 6 kenan suna zanga zanga ta neman shugaban kasar Harry Rogua Rimpianina ya sauka kan kujerar shugabancinn kasar. Saboda dokar da majalisar dokokin ta amince a cikin kwanakin baya wanda a fahintarsu an kafata ne don hana dan takararsu Mark Ravalomana tsayawa takarar shugabancin kasar a cikin zabe mai zuwa.