Karon Farko, Sojoji Da 'Yan Sanda Na Zabe A Tunisia
A karon farko 'yan sanda da sojoji a Tunisia na kada kuri'a a tarihin kasar, a yayin zaben farko na wakilan kananan hukumomi tun bayan boren 2011.
Wani jami'in 'yan sanda da ya kada kuri'a a zaben na yau Lahadi, ya shaida wa masu aiko da rahotanni cewa wannan rana mai cike da tarihi, suna zabe kamar ko wanne dan kasa.
A lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Ben Ali, hukumomi sun haramta wa 'yan sanda da sojoji kada kuri'a a zabe, don a cewarsu su nisanta daga harkokin da suka shafi siyasa.
Amma bayan boren 2011 wanda ya kai samar da kungiyoyin 'yan sanda, inda suka bukaci 'yancin kada kuri'a.
Saidai dokar ta ta'alaka ne kawai ga 'yancin kada kuri'a a zaben wakilan kananan hukumomi kawai, ga 'yan sandan da kuma sojoji.