Majalisar Kasar Chadi Ta Amince Da Sabon Kundin Tsarin Mulkin Kasar
(last modified Tue, 01 May 2018 05:26:33 GMT )
May 01, 2018 05:26 UTC
  • Majalisar Kasar Chadi Ta Amince Da Sabon Kundin Tsarin Mulkin Kasar

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka yiwa kwaskwarima wanda zai ba wa shugaban kasar Idris Derby daman ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2033 a kan karagar mulki, lamarin da 'yan adawan kasar suka yi watsi da shi.

Kafar watsa labaran Africanews ta bayyana cewar a kuri'ar da aka kada  a majalisar dokokin na Chadi da 'yan adawa suka kaurace wa zaman, ‘yan majalisa 132 ne suka kada kuri’ar amincewa da yiwa kundin tsarin mulkin gyara, yayin wasu biyu kacal ne suka ki amincewa da hakan.

A bisa sabon kundin tsarin mulkin dai an sake dawo da batun kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa zuwa ga wa'adin mulkin biyu wanda aka cire a kuri'ar jin ra'ayin al'ummar kasar da aka gudanar a shekara ta 2005, wanda hakan yana nufin kenan shugaba Deby din zai iya sake ci gaba da mulkin kasar har na wa'adin mulki biyu na shekaru shida-shida a nan gaba bayan wa'adin mulkinsa na yanzu ya kare a shekara ta 2021.

Masu adawa da shugaba Deby din dai sun ce sabon kundin tsarin mulkin, wanda a cikinsa aka cire matsayin firayi minista da kuma gabatar da tsarin shugaban kasa mai cikakken iko, wani shiri ne na tabbatar da shugaba Deby din a matsayin wani sarkin gargajiya mai mulki irin na kama-karya.

A shekarar 1990 ne dai shugaba Derby din ya dare karagar mulkin kasar Chadi bayan jagorantar 'yan tawayen kasar da suka kifar da gwamnatin wancan lokacin.