Matsalar Inji Ce Musababin Faduwar Jirgin Saman Soji A Aljeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3052-matsalar_inji_ce_musababin_faduwar_jirgin_saman_soji_a_aljeriya
Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da mutuwar sojojin kasar 12 sakamakon faduwar jirgin sama kirar helikobta mallakin rundunar sojin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 28, 2016 06:31 UTC
  • Matsalar Inji Ce Musababin Faduwar Jirgin Saman Soji A Aljeriya

Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da mutuwar sojojin kasar 12 sakamakon faduwar jirgin sama kirar helikobta mallakin rundunar sojin kasar.

Mataimakin ministan tsaro kuma shugaban rundunar sojin kasar Aljeriya Ahmad Qayid Salah a yau Litinin ya fitar da sanarwar cewa: Jirgin saman sojin rundunar kasar kirar helikobta da ya fadi a jiya Lahadi, jirgin saman ya samu matsalar inji ne lamarin da ya janyo faduwarsa a yankin kudu maso yammacin kasar ta Aljeriya tare da hasarar rayukan sojoji goma sha biyu.

Ahmad Salah ya kara da cewa; Tun bayan faduwar jirgin saman a jiya suka bada umurnin fara gudanar da bincike kan musabbabin faduwarsa, amma zuwa yanzu dai rahoton da ke hannu yana nuni da cewa matsala ce ta inji.