Kudaden Libiya : An Bukaci Shugabannin Afrika Su Yi Bayyani
Wasu kungiyoyin fara hula a Nijar da Congo sun bukaci shugabanin kasashensu dasu yi bayyani kan kudaden da gwamnatin Libiya ta ce tsohon shugaban kasar mirigayi Muammar Ghaddafi ya ranta masu.
A kwanan nan ne dai shugaban gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya, Fayez al-Sarraj ya ce kasarsa za ta bi diddigin kudaden da tsohon shugaban kasar Ghaddafi ya ranta wa wasu kasasen Afrika dana Larabawa.
Kimanin kudade da yawansu ya kai Dalar Amurka Bilyan 67 ne gwamnatin Libiyar ke sa ran amsowa a kasashen da suka hada da Afrika ta Kudu, Tanzania, Zambia, Ivory Coast da Nijar da kuma Uganda.
Kawo yanzu babu wani martani daga wata kasar Afrika da aka ambato cikin jerin kasashen da aka ranta wa kudaden, amma wasu kungiyoyin fara hula a kasar Nijar irinsu MPCR, ta bukaci shugaban kasar da ya bi diddigin labarin, don sanin ko nawa aka ranta wa kasar, sannan a mayar wa da Libiyar kudadenta idan ta tabbata.