Mali : An Tsaida Shugaba IBK A Matsayin Dan Takaran Shugaban Kasa
(last modified Mon, 07 May 2018 05:49:52 GMT )
May 07, 2018 05:49 UTC
  • Mali : An Tsaida Shugaba IBK A Matsayin Dan Takaran Shugaban Kasa

A Mali, wasu jam'iyyun siyasa su guda 70, sun tsaida Shugaban kasar mai ci Ibrahim Bubakar Keita, a matsayin dan takara shugaban kasa a zaben kasar mai zuwa.

Jam'iyyun sun bayyana hakan ne a wani babban taronsu jiya a Bamako babban birnin kasar ta Mali, duk da cewa shi Shugaban kasar Ibrahim Keita bai bayyana matsayinsa ba kan ko zai tsaya takarar a zaben na ranar 29 ga watan Yuli mai zuwa ba.

A shekara 2013 ne aka zabi Ibrahim Bubakar Keita dan shekaru 73, a wa'adin mulki na shekaru biyar, kuma wasu majiyoyin sun ce yana da niyyar sake tsayawa takara ta neman wa'adi na biyu.

kawo yanzu dai gomman 'yan takara ne suka bayyana aniyyarsu ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar, cikinsu kuwa da akwai wani tsaohon fira minista da kuma wasu tsaffin ministoci.