An Koma Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Juyin Mulki A Burkina Faso
(last modified Wed, 09 May 2018 14:42:23 GMT )
May 09, 2018 14:42 UTC
  • An Koma Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Juyin Mulki A Burkina Faso

A Burkina Faso an koma shari'ar wandanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a watan Satumba na shekara 2015 bayan dage zaman sau da dama.

Mutanen sun hada da wasu manyan janar biyu, wato Gilbert Diendere da kuma Djibril Bassole, wadanda na hannun daman tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ne.

Baya gare su da akwai kuma mutane kimanin 80 da ake zargi da cin amanar kasa, kisa, raunanawa da kuma lalata dukiyar kasa. 

Wasu majiyoyin shari'a sun ce wadanda ake zargin na iya fuskantar hukunci mai tsanani a yayin shari'a da za'a kwashe watanni ana yi.

A watan Afrilun da ya gabata, gomman kungiyoyin fara hula ne a kasar ta Burkina faso sun kira masu shari'a da suyi duk iya kokarinsu don ci gaba da gudanar da wannan shari'ar.