Nijar Ta Tisa Keyar 'Yan Sudan 140 Zuwa Libiya
Hukumomi a jihar Agadas dake arewacin jamhuriya Nijar, sun tisa keyar 'yan gundun hijira Sudan 140 zuwa yankin Madama a iyaka da Libiya, bisa dalilai na tsaro.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan samamen da 'yan sanda suka kai a wuraren da 'yan gudun hijira suke da zama.
Mutanen dai na daga cikin gungun 'yan gundun hijira da suka shiga kasar daga Libiya, don neman mafaka.
Kimanin 'yan Sudan da Chadi 2,000 ne suka shiga jihar ta Agadas a baya bayan nan, saidai bisa fargabar da jama'ar yankin suke da ita kan yanayin tsaron lafiyar iyalansu suka bukaci hukumomin yankin dasu dauki mataki.
Babbar fargabar da mutanen yankin suke da ita, shi ne cewa mafi akasarin wadanda suka fito daga Libiyar sun lakanci aiki da bindigogi.
Hukumar kula da bakin haure a yankin dai ta nuna damuwa akan matakin hukumomin, inda ta ce tana iya kokarinta na ganin ta taimaka wa wadanda 'yan gudun hijira dake cikin bukata musamman yara da mata.