An Kashe Wani Jami'in Diplomasiyyar Nijeriya A Kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30728-an_kashe_wani_jami'in_diplomasiyyar_nijeriya_a_kasar_sudan
Majiyoyin tsaron kasar Sudan sun bayyana cewar wasu mutane da ba a riga da an tantance su ba sun kashe wani jami'in diplomasiyyar Nijeriya a kasar ta Sudan a safiyar yau Alhamis.
(last modified 2018-08-22T07:01:49+00:00 )
May 11, 2018 13:42 UTC
  • An Kashe Wani Jami'in Diplomasiyyar Nijeriya A Kasar Sudan

Majiyoyin tsaron kasar Sudan sun bayyana cewar wasu mutane da ba a riga da an tantance su ba sun kashe wani jami'in diplomasiyyar Nijeriya a kasar ta Sudan a safiyar yau Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar wasu majiyoyin tsaron kasar Sudan din sun bayyana masa cewa a safiyar yau ne aka samu gawar wani jami'in diplomasiyyar Nijeriya da ke kasar ta Sudan a gidansa bayan da wasu suka kashe shi.

Majiyar tsaron ta ce daga dukkan alamu wasu mutane ne suka kashe jami'in diplomasiyyar wanda har ya zuwa yanzu dai ba a bayyana sunansa ba, sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike don ya zuwa yanzu ma an kama wasu mutane da ake zargi da hannunsu cikin lamarin kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.