Somaliya: Harin Ta'addanci Ya Kashe Mutane 4
(last modified Sun, 13 May 2018 12:00:35 GMT )
May 13, 2018 12:00 UTC
  • Somaliya: Harin Ta'addanci Ya Kashe Mutane 4

Bom din ya tashi ne a wani yanki a kusa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na tarayyar Afirka da ke kudancin kasar.

Majiyar tsaro daga Somaliya ta ce; Baya ga mutane hudu da su ka mutu, sai kuma wasu biyar da su ka jikkata.

Kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai an fi danganta hare-hare irin wadannan da kungiyar al-Shabab.

Fiye da shekaru 20 kenan kasar ta Somaliya take fama da rashin tsaro, saboda rashin tsayayyar gwamnati mai karfi.

Kungiyar al-shabab tana a matsayin babbar barazana ga kasar da kuma kasashen makwabta.