OCHA : Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutane 220,000 Da Muhallansu A Somaliya
Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD ya bayyana cewa, kimanin mutane dubu dari biyu da ashiri ne, suka rasa matsugunansu, sakamakon barnar da kogunan Juba da Shabelle ke ci gaba da yi bayan da suka tumbatsa biyo bayan ruwan sama mai karfin gaske da aka tabka.
Mataimakin kakakin hukumar ta OCHA Jens Laerke, ya bayyanawa zaman MDD cewa, ambaliyar ta shafi mutane 718,000 a yankin arewa maso gabashin Afirka, yayin da mutane 132 suka mutu a Kenya.
Mista Laerke ya ce, abokan hulda masu gudanar da ayyukan jin kai da hukumomi Somaliya suna samar da kayayyakin jin kai, da kuma kayan aiki, don gyara gabobin kogin da suka lalace.
Wasu bayanai sun ce akwai barazanar ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa a wasu yankunan kasar kasar Habasha.
A watan Afrilu kadai, kimanin mutane 171,000 ne suka rasa matsugunansu a sassan kasar, galibi saboda ambaliyar da ta faru a yankin Somaliya.