WHO : Annobar Ebola Bata Kai Matsayin Barazana Ga Duniya Ba
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce annobar cutar Ebola data bulla a Jamhuriya Demokuraddiyar Congo, bata kai matsayin babbar barazana ga duniya ba, kasancewar ana da halin murkushe cutar ta hanyar matakan da aka dauka wandanda suka hada da allurar riga kafi.
Saidai kwamitin gaggawa na hukumar da ya taru a birnin Geneva, ya ce kasashe tara dake makobtaka da RDC, cikin har da Congo-Brazaville, da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, an sanar da su cewa suna fuskantar babbar barazanar yaduwar cutar.
A saboda haka hukumar ta WHO ta ce ta gayyaci kasashen 9 dake makobtaka da Jamhuriya Demokuraddiyar Kongon, a daura da babban taronta da za'a fara a ranar Litini mai zuwa a Geneva.
Kawo yanzu dai adadin mutaten da mahaikaciyar cutar mai zubar da jini ta Ebola ta kashe a Jamhuriya Demokuraddiyar Kongo, sun kai 25, cikin jimmilar 45 da aka tabbatar ko kuma ake tsammanin sun kamu da cutar a cewer hukumar ta WHO.