Somalia Ta Musanta Tattaunawa Da Kenya Kan Iyakokin Ruwa Na Kasashen biyu
Ministan harkokin wajen kasar Somalia ya musanta labaran da aka watsa na cewa kasarsa da kasar Kenya makobciya sun tattauna batun kan iyakokin kasashen biyu na kan cikin ruwa.
Kamfanin dillancin labarab Fars na kasar Iran ya nakalto Ahmad Isaah Awad yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa, za'a maida batun takaddama kan iyakokin kasashen biyu na cikin ruwa ga kotun kasa da kada don warware ta. Kafin haka dai ministan harkokin wajen kasar Kenya Monika Juma ta fadawa majallar New Afrika a wata hiran da ta hadasu kan cewa kasashen Kenya da Somalia sun sami hanyar warware takaddamar iyakokin kasashen biyu na cikin ruwa.
A lokacin tsohon shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mahamoud ne takaddama kan iyakokin kasashen Somalia da Kenya ta kunno kai ta kuma yi tsanani tsakanin kasashen biyu.