Zimbabwe : Majalisa Za Ta Saurari Mugabe Kan Batan Kudadin Lu'u-Lu'u
(last modified Wed, 23 May 2018 05:50:21 GMT )
May 23, 2018 05:50 UTC
  • Zimbabwe : Majalisa Za Ta Saurari Mugabe Kan Batan Kudadin Lu'u-Lu'u

A Zimbabwe, yau Laraba ne ake sa ran kwamitin majalisar dokokin kasar mai kula da harkokin ma'adunai da makamashi, zai saurari tsohon shugaban kasar Robert Bugabe kan badakalar salwantar wasu kudaden rara na lu'u-lu'u da yawansu ya kai Dalar Amurka Bilyan 15.

Saidai ofishin tsohon shugaban kasar, bai tsaida magana ba kan cewa, Mugaban zai halarci zaman ba ko kuma A'a, a cewar shugaban kwamitin majalisar Temba Mliswa. 

Babban abu shi ne dai mun cika alkawari na gayyatarsa a cewar Mista  Temba, sannan a cewarsa binciken ba wai yana nufin bita da kulin siyasa ne ba, kawai don neman haske ne kan amfani da dukiyar kasa.

Dama kafin tsohon shugaban kasar, kwamitin ya saurari wasu ministocin kasar da dama, da manyan jami'an tsaro dana ma'aikatun ma'adanai na kasar.