MDD Ta Taimaka Wa Kasashen Sahel Dake Fama Da Fari
Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, ya samar da dala miliyan talatin, ga wasu kasashen yankin Sahel hudu wadanda ke fuskantar matsanancin fari da tsadar kayayakin abinci da kuma tabarbarewar tsaro.
Rahoton da ofishin ya fitar ya nuna cewa yaran kimanin miliyan 1.6 ne ke cikin hadarin kamuwa da matsananciyar tamowa, inda mutane miliyan 5 kuma ke bukatar abinci da taimakon abun da za su dogara da shi, a wannan yanayi da ake tsammanin na gab da zama lokacin bazara mafi muni, idan abincin da aka adana ya kare kafin lokacin girbi na gaba.
Kudin da aka fitar daga asusun ba da daukin gaggawa na duniya, zai ba hukumomin ba da agaji damar kai wa ga mutanen da matsalar ta fi shafa, musammam a yankunan da ake noma da kuma kiwo da noma, a kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da kuma Mauritania.
Jimilar dala biliyan 1.37 ne ake bukata don taimakawa mutanen da suka fi rauni, a yankunan da farin ya shafa a Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Senegal.