Ma'aikata Sun Sake Kiran Yajin Aikin Gama-Gari A Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31170-ma'aikata_sun_sake_kiran_yajin_aikin_gama_gari_a_chadi
Kungiyoyin kwadago a kasar Chadi sun sake kiran wani yajin aikin gama gari daga ranar litinin mai zuwa domin bukatar gwamnatin kasar ta biya su bashin kudaden alawus din su da aka zabtare.
(last modified 2018-08-22T07:01:53+00:00 )
May 27, 2018 06:14 UTC
  • Ma'aikata Sun Sake Kiran Yajin Aikin Gama-Gari A Chadi

Kungiyoyin kwadago a kasar Chadi sun sake kiran wani yajin aikin gama gari daga ranar litinin mai zuwa domin bukatar gwamnatin kasar ta biya su bashin kudaden alawus din su da aka zabtare.

Da yake bayyana hakan a wani taro jiya Aasabar, mai Magana da yawun kungiyoyin kwadagon, Michel Barka, ya ce yajin aikin zai fara daga ranar litinin.

Barka yace ma’aikatan asibiti zasu yi yajin aikin tare da jalalo domin kulawa da marasa lafiya.

Ma’aikatan na bukatar gwamnati ta biya su kudaden alawus din su da aka zabtare daga watan Janairu, amma shugaban kasar Idris Deby Itmo ya bukaci su yi hakuri har zuwa karshen shekara.