Uganda Ta Musunta Bullar Ebola A Kasar
(last modified Mon, 28 May 2018 11:10:16 GMT )
May 28, 2018 11:10 UTC
  • Uganda Ta Musunta Bullar Ebola A Kasar

Gwamnatin Uganada ta musunta rahotannin cewa an samu bullar cutar Ebola a cikin kasarta.

A game da jita- jitan dake yaduwa a shafukan sada zumunta, ministar lafiya ta kasar ta ce an kwantar da wani mutum dan shekaru 35 a babban asibitin Kakumiro dake yammacin kasar, wanda yake fama da zazzabi mai tsanani tare da zubar da jini da amai, wanda ya rasu daga baya.

Kuma binciken da akayi akansa ya nuna ba cutar Ebola ce ba.

Alkalumman da hukumar lafiya ta duniya ta fitar, sun nuna cewa mutum 56 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola tun bayan bullatar a Jamhuriya Demokuraddiyar Kongo.