Alkalai Sun Shiga Yajin Aiki Na Kwanaki Uku A Tchadi
(last modified Tue, 29 May 2018 18:58:29 GMT )
May 29, 2018 18:58 UTC
  • Alkalai Sun Shiga Yajin Aiki  Na Kwanaki Uku A Tchadi

Alkalan kasar Tchadi sun shiga yajin aiki na kwanaki uku domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda jami'an tsaro suka kaiwa wani lauya farmaki a kudancin kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya litinin alkalan kasar Tchadi sun shiga yajin aiki na kwanaki uku domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda jami'an tsaron suka kai farmaki kan wani lauya mai suna Doumara Manasseh da wadanda yake wakilta uku a garin Doba na kudancin kasar.

Bayan duka da zaki da suka yiwa wadanda lauya Doumara Manasseh yake wakilta , jami'ar tsaron sun isa da su zuwa ga ofishin 'yan sanda na garin Doba a makon da ya gabata.

A nasa bangare, lauya Manasseh ya bukaci gwamnati ta sauke shugaban 'yan sandar na garin Doba sannan kuma ta gurfanar da shi a gaban shari'a domin ya amsa tuhumar da ake yi masa, wanda hakan ya sanya alkalan kasar shirya gudanar da zanga-zangar lumana a wannan talata, amma gani cewa ba su samu izini daga gwamnati ba, sun takaita da kirar taron manema labarai.

A makon da ya gabata, alkalan garin Doba sun kudiri rufe kotun jihar saboda barazanar rashin tsaro da suke fuskanta.