Babban Sakataren MDD Na Ziyara A Mali
(last modified Wed, 30 May 2018 06:59:41 GMT )
May 30, 2018 06:59 UTC
  • Babban Sakataren MDD Na Ziyara A Mali

Babban sakataren Majalisar dinkin duniya Antonio Guteres ya isa birnin Bamako babban birnin kasar Mali a jiya Talata a ziyarar kwanaki biyu da zai gudanar a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa bayan isarsa kasar Mali a jiya ya halarci bikin ranar dakarun tabbatar da zaman lafiya a sansanin sojojin MINUSMA, wato dakarun Majalisar dinkin duniya da suke aikin tabbatar da zama lafiya a arewacin kasar Mali tun shekara ta 2013. 

A cikin ziyararsa ta kwanaki biyu a kasar ta Mali, ana saran babban sakataren zai gana da shugaban kasa Ibrahim Bubakar Kaita, wasu kungiyoyin matasa da na mata da kuma wasu manya manyan jami'an gwamnatin kasar. Har'ila yau ziyarar Antonio Guteres ta zo ne a dai dai lokacin da shugaban kasar ta Mali Ibrahim Kaite ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takatar shugaban kasa karo na biyu wanda za'a gudanar a cikin rani na wannan shekara. 

Kasar Mali dai tana fama da matsalolin tsaro tun bayan juyin mulkin da sojoji suka gudanar a kasar a shekara ta 2012 wanda ya bawa yan ta'adda damar kwace iko da arewacin kasar na wani lokaci.