Zimbabwe : Za'a Yi Zabe A Ranar 30 Ga Wata Yuli
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31274-zimbabwe_za'a_yi_zabe_a_ranar_30_ga_wata_yuli
Zimbabwe, za ta shirya manyan zabukanta na farko tun bayan kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.
(last modified 2018-08-22T11:31:54+00:00 )
May 30, 2018 10:54 UTC
  • Zimbabwe : Za'a Yi Zabe A Ranar 30 Ga Wata Yuli

Zimbabwe, za ta shirya manyan zabukanta na farko tun bayan kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.

Za'a gudanar da zabukan ne da suka hada dana shugaban kasa, gami dana 'yan majalisar dokoki da kuma wakilan kananan hukumomi a ranar Litini 30 ga watan Yuli mai zuwa.

Za'a kuma je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa idan ta kama a ranar 8 ga watan Satumba. 

Shugaban kasar mai ci, Emmerson Mnangagwa, na takara a karkashin inuwar jam'iyyar Zanu Pf dake mulkin kasar tun bayan samun 'yancin kanta a 1980.