Fira Ministan Tunusiya Ya Dauki Alkawarin Gudanar Da Gyare-Gyare A Kasarsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31284-fira_ministan_tunusiya_ya_dauki_alkawarin_gudanar_da_gyare_gyare_a_kasarsa
Fira ministan Tunusiya ya ce: Tabbas gwamnatinsa tana fuskantar matsaloli a fagen gudanar da ayyukanta sakamakon haka dole ne ya dauki matakin gudanar da gyare-gyare da nufin bunkasa ci gaban kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:54+00:00 )
May 30, 2018 19:37 UTC
  • Fira Ministan Tunusiya Ya Dauki Alkawarin Gudanar Da Gyare-Gyare A Kasarsa

Fira ministan Tunusiya ya ce: Tabbas gwamnatinsa tana fuskantar matsaloli a fagen gudanar da ayyukanta sakamakon haka dole ne ya dauki matakin gudanar da gyare-gyare da nufin bunkasa ci gaban kasar.

Fira minista Yusuf Shahid ya yi furuci da cewar gwamnatinsa tana fuskantar matsalolin siyasa da na tattalin arziki, to amma dai a fili yake cewa babu wata gwamnati da zata bugi kirji tace bata da wata matsala a fagen gudanar da kasa, don haka zai yi iyaka kokarinsa na ganin ya gudanar da gyare-gyare domin shawo kan wasu matsalolin.

Shahid ya kara da cewa: Kafin karshen wannan shekara ta 2018 zai bullo da wasu sabbin tsare-tsare da zasu haifar da gyare-gyare a cibiyoyin gwamnatin Tunusiya musamman a asusun kyautata harkar lafiya da kuma batun matsalar albashin ma'aikatan gwamnatin kasar.

Gwamnatin fira minista Yusuf Shahid dai tana fuskantar kakkausar suka daga 'yan adawar kasar musamman a fagen gazawar da ta yi wajen magance matsalar harkar tattalin arziki gami da matsin lamban da take fuskanta kan yin murabus.