Libiya Ta Mayar Da 'Yan Ci-Rani 221 Kasashensu
May 31, 2018 10:04 UTC
Mahukunta a Libiya, sun sanar da tisa keyar 'yan ci rani 'yan asalin kasashen Afrika dana Asiya su 221 zuwa kasashensu.
Wannan dai a cewar mahukuntan na daga cikin tsarin mayar da 'yan ci ranin dake bukata kasashensu na hadin gwiwa da hukumar kula da bakin haure ta MDD.
163 daga cikin 'yan ci ranin 'yan asalin kasar Somaliya ne, da aka mayar dasu gida ta hanyar jirgin sama.
Sauren kuma sun hada da 'yan Bangaladesh talatin, da kuma wasu na Pakistan 28, wadanda su ma aka mayar dasu kasashensu na asali.
Tags