Mali : 'Yan Sanda Sun Murkushe Masu Zanga-zanga A Bamako
(last modified Sun, 03 Jun 2018 05:53:07 GMT )
Jun 03, 2018 05:53 UTC
  • Mali : 'Yan Sanda Sun Murkushe Masu Zanga-zanga A Bamako

'Yan sanda a Mali, sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma lulake, wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Bamako babban birnin kasar.

Rahotanni daga Malin sun ce an samu mutane da dama da suka raunana a zanga-zangar da hukumomi suka haramta, a yayin da 'yan adawa ke cewa mutanansu da suka raunana sun kai kimanin 30.

'Yan adawa a kasar sun bukaci fira ministan kasar, Sumeylu Bubeye Maiga, da ya yi murabus, daga mukaminsa, sakamakon yadda 'yan sanda sukayi amfani da karfi kan masu zanga zangar.

Wannan zanga-zanga dai na zuwa ne a yayin da zaben shugaban kasar ta Mali na watan Yuli ke karatowa.

Babban sakatare na MDD, Antonio Guteress, ya ce ya damu matuka dangane da halin da ake ciki a kasar ta Mali inda ya kai ziyara a kasrhen watan Mayu da ya shude, inda ya bukaci bangarorin da batun ya shafa dasu kai zuciya nesa, da kuma samar da hanyoyin da zasu kai ga gudanar da sahihin zabe a kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.