Aljeriya Ta Kira Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai.
Ma'aikatar harakokin wajen kasar Aljeriya ta kira jakadan kungiyar tarayyar Turai dake cikin kasar domin bayyana rashin jin dadinta game da wani faifan video na cin mutuncin Shugaban kasar Abdul-Azez Boutelfika.
Kamfanin dillancin labaran Pars ya nakalto ma'aikatar harakokin wajen kasar Aljeriya cikin wani bayyani da ta fitar a jiya Lahadi ta ce ta dauki wannan matakin ne domin nuna rashin amincewar kasar da wani faifai video da aka nuna a hedkwatar majalisar kungiyar Turai dake birnin Brussels, inda a ciki aka nuna cewa Shugaba Boutelfika na kasar Aljeriya ba shi da lafiya kuma na kusa da shi su suke tafiyar da al'amuran kasar.
Layla Haddad tsohuwar ma'aikaciyar gidan talbijin din Aljazeera kuma daraktar tashar talbijin din CNB News a Brussels ita ce ta wallafa wannan video.
Ofishin jakadancin kasar Aljeriya a birnin Brussels ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda aka watsa faifan video a kafafen sadarwa na zamani, inda ya ce an yi amfani da 'yan jaridar Aljeriya domin taimakawa kasashen waje da masu adawa da kasar ta Aljeriya.
Tun a shekarar 1999 ne shugaba Boutelfika mai shekaru 81 a duniya yake riki da ragamar shugaban kasar ta Aljeriya.
A nasu bangare 'yan adawa a kasar sun bukaci Shugaban yayi murabus, ganin cewa ba shi da cikekkiyar lafiyar da zai iya ci gaba da jan ragamar kasar.