Mayakan Al-Shabab Sun Kashe Yan Majalisar Dokokin Somalia 2
(last modified Wed, 06 Jun 2018 19:09:02 GMT )
Jun 06, 2018 19:09 UTC
  • Mayakan  Al-Shabab Sun Kashe Yan Majalisar Dokokin Somalia 2

Mayakan kungiyar alshabab a kasar Somalia sun kashe yan majalisar dokokin kasar guda biyu a wani harin da suka kai masu a wajen birnin Magadishi babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa yan majalisar guda biyu tare da maso rakiyansu sun mutu ne a lokacin da suke je garin Bal'ad , kilomita 30 daga babban birnin kasar Magadishu a safiyar yau Laraba. A can ne mayakan na Al-shabab suka farwa tawagar suka kuma kashe yan majalisar guda biyu da kuma dukkan masu rakiyansu su 10.

Labarin ya kara da cewa a mayakan na al-shabab sun kashe wani dan majalisar a wajen birnin na Magadishu a cikin watan da ya gabata.

Kungiyar Al-shabab dai tana iko da wani bangare na kasar Somalia tun shekara ta 2011. Duk da cewa dubban dakarun tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar dinkin duniya suna aikin tabbatar da zaman lafiya a klasar amma tasirinsu kadan ne idan an fita daga babban birnin kasar Magadishi.