An Kori Ministan Cikin Gidan Tunisia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31502-an_kori_ministan_cikin_gidan_tunisia
A Tunisia, an kori ministan cikin gidan kasar, Lotfi Brahem, daga gwamnati.
(last modified 2018-08-22T11:31:56+00:00 )
Jun 07, 2018 05:46 UTC
  • An Kori Ministan Cikin Gidan Tunisia

A Tunisia, an kori ministan cikin gidan kasar, Lotfi Brahem, daga gwamnati.

Gwamnatin kasar dai bata yi karin bayyani ba, akan dalilin korar ministan, amma matakin ya zo kwanaki kadan da wani kwale-kwale dauke da bakin haure ya nutse a gabar ruwan kasar ta Tunisia.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce tuni Fira ministan kasar, Youssef Chahed, ya nada ministan shari'a, Ghazi Jeribi, a mukamin na ministan cikin gida.

Ko baya ga ministan cikin gidan kasar, an kuma sallami wasu ma'aikata goma, ciki har da wasu jami'ai a rundinar gardi-sarki dake a yankin Kerkennah dake gabashin kasar inda kwale-kwalen ya nuste.

Kawo yanzu dai an tsamo gawarwakin mutum 48, bayan aukuwar lamarin, a cikin daren ranar Asabar, kuma mafi yawan wadanda suka mutun 'yan asalin kasar ta Tunisia ne.