Mutane 16 Sun Mutu A Wani Harin Ta'addanci A Tsakiyar Mali
Jun 09, 2018 18:07 UTC
Ma'aitakar tsaro a Mali ta ce an kashe sojojinta uku da kuma jikkata wasu uku na daban a wani harin ta'addanci da aka kai kan wani sansanin soji da yankin Boni a tsakiyar kasar.
Maharan sun dai kai harin ne da rokoki da safiyar yau Asabar, a cewar kakakin rundinar sojin kasar ta Mali, kuma sojojin kasar sun yi nasara dakile harin.
Sanarwar ta ce an kashe mahara 13, a musayar wutar da aka kwashe sa'o'i ana yi bayan kaddamar da harin.
Sojojin sun kuma kwato makamman yaki masu yawa da suka hada da ababe masu fashewa.
Kakakin rundinar sojin kasar, Kanal Diarran Koné, ya ce sojojin sun maid amartani nan take.
Tags