An Ceto Bakin Haure Sama Da 470 A Gabar Ruwan Maroco
Sojojin Maroco sun sanar da ceto bakin haure dake son zuwa kasashen sama da 470 a gabar ruwan kasar
Hukumar gidan radio da talabijin na kasar Iran ta nakalto Sojojin Maroco na cewa a jiya asabar, jami'an tsaron ruwan sun samu nasarar ceto bakin haure dake son zuwa kasashen turai ta barauniyar hanya 472, daga cikinsu akwai Mata 28 da kuma kananen yara 27 a gabar ruwan kasar.
Saidai sanarwar ta Sojojin kasar Marocon ba su karin haske ba kan bakin haure da ake ceto kan kasashen da suka fito.
Ko wata shekara duban 'yasashen Afirka ne ke bi ta kasar Maroco ta hanyar amfani da ruwan kasar domin zuwa kasar Aspaniya, to saidai mafi yawa daga cikinsu suna fuskantar matsala a kan hanyar.
A cikin shekarun baya-bayan 'yan gudun hijrar sun canza hanya a kokarin da suke yi na zuwa kasashen Turai daga kasar Libiya zuwa kasar Maroco, sakamakon tarnakin da suke fuskanta a kasar ta Libiya.