Nijar Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Ciniki Marar Iyaka Ta Afrika
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31610-nijar_ta_rattaba_hannu_kan_yarjejeniyar_ciniki_marar_iyaka_ta_afrika
Jamhuriyar Nijar ta sanya hannu kan takardun kungiyar tarayyar Afrika AU na yarjejeniyar ciniki marar iyaka tsakanin kasashen nahiyar Afrika wato (AFCFTA) a takaice.
(last modified 2018-08-22T11:31:57+00:00 )
Jun 11, 2018 06:22 UTC
  • Nijar Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Ciniki Marar Iyaka Ta Afrika

Jamhuriyar Nijar ta sanya hannu kan takardun kungiyar tarayyar Afrika AU na yarjejeniyar ciniki marar iyaka tsakanin kasashen nahiyar Afrika wato (AFCFTA) a takaice.

Shugaban gudanarwa na kungiyar (AU), Musa Faki Mahamat, ne ya sanar da hakan, inda kuma ya bukaci ragowar mambobin kasashen wadanda har yanzu ba su sanya hannu kan yarjejeniyar ba da su hanzarta amincewa da yarjejeniyar.

A watan Maris da ya gabata, kimanin mambobin kasashen kungiyar ta (AU) 44 ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar AfCFTA a lokacin taron kolin AU a Kigali na kasar Rwanda, kana kasashe 31 suka rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyar da ta shafi zirga zirgar mutanen nahiyar cikin 'yanci, da 'yancin izinin zama da kuma 'yancin kafa tsarin cinikayya na bai daya.

Ana bukatar a kalla kasashen 22 su amince da yarjejeniyar, inda kawo yanzu, kasashe 4 ne da suka hada da Ghana, Kenya, Nijar, da Rwanda ne kawai suka riga sun amince da yarjejeniyar ta (AfCFTA).