Sojin Najeriya Sun Hallaka 'Yan Boko Haram 23
Majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce sojojin kasar sun hallaka 'yan mayakan kungiyar Boko haram 23 a wani farmaki da suka kai a yankin tafkin Chadi.
Da yake bayyana hakan a wata hira da kamfanin dilancin labaren Xinhua, kakakin rundinar sojin Najeriyar, Texas Chukwu, ya ce mayakan na boko haram masu yawa sun tsere bayan da aka raunanasu.
Kakakin rundinar sojin Najeriyar, ya ce a farmakin na hadin gwiwa da aka kai tare da dakarun Kamaru, an kuma kwato tarin makamai da 'yan boko haram din suka yi amfani dasu.
A ranar 15 ga watan Mayu da ya gabata ne rundinar sojin Najeriya ta kaddamar da wani gagarimin farmaki da za'a kwashe watanni hudu anayi da nufin murkushe kungiyar ta Boko haram a yankin tafkin Chadi.
Alkalumma dai sun nuna cewa mutane samda da 20,000 ne suka rasa rayukansu, kana wasu miliyan 2,3 suka rasa muhallansu tun dai bayan da kungiyar boko haram ta soma kai hare harenta a Najeriya a cikin shekara 2009.