'Yan Takara 23 Zasu Fafata A Zaben Zimbabwe
A Zimbabwe 'yan takara 23 ne suka yi rejista a takara zaben neman shugabancin kasar na ranar 30 ga watan Yuli dake tafe, ciki har da shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa.
A jiya ne dai 'yan takara zabukan kasar da suka hada dana shugaban kasa, 'yan majalisu da wakilan kananan hukumomi suka ajiye takardun takararsu gaban wasu kotunan kasar.
Bayan tantancewa ne hukumar zaben kasar (ZEC), ta bayyana amuncewa da takara mutum 23 da zasu fafata a zaben shugaban kasar, sabanin guda biyar da suka fafata a zaben shugabancin da ya gabata na 2013.
Mista Nelson Chamisa, na jam'iyyar (MDC), wanda ya maye gurbin jagoran 'yan adawa na kasar Morgan Tsvangirai, wanda ya rasu a watan Fabariru da ya gabata shi ne ake wa kallon babban dan hammaya na daga cikin 'yan takarar da zasu fafata a zaben, sai kuma tsohuwar mataimakiyar tsaohon shugaba Robert Mugabe, cewa da Joice Mujuru wacce ya kora a 2014.
Tuni dai wasu daga cikin 'yan takarar irinsu Violet Mariyacha, suka fara nuna damuwa akan sahihancin zaben dake tafe, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, ya mika mulki bisa matsin lambar sojojin kasar da jam'iyyarsa ta Zanu PF.