Najeriya : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 31 A Borno
(last modified Sun, 17 Jun 2018 16:16:31 GMT )
Jun 17, 2018 16:16 UTC
  • Najeriya : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 31 A Borno

Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake biyu da ake danganta wa dana kungiyar Boko Haram a shiyar arewa maso gabashin kasar.

Bayanai daga yankin sun ce an kai hare haren ne da yammacin jiya Asabar, a garin Damboa dake jihar Borno, a daidai lokacin da jama'a ke dawowa daga bukukuwan karamar Sallah.

Wani jami'i a yankin da bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya karu, kasancewar akwai dayewa da suka ji munannen raunuka.

Wasu bayanai na daban sun ce bayan hare haren kunar bakin waken an kuma kai hari da gurneti a daidai lokacin da jama'a suka taru a wurin, koda yake wasu sun ce harin roka ne.

Ko a ranar 1 ga watan Mayun da ya gabata ma, an kai wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a wani masallaci da kuma wata kasuwa a garin Mubi dake jihar Adamawa inda mutane 86 suka rasa rayukansu. 

Rikicin Boko Haram da aka shafe shekaru tara ana yi, ya dai yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 tare da tilasta wa wasu kimanin miliyan 2,6 kaurace wa muhallansu.