Rasha 2018: Senegal Ta Doke Poland A wasan Cin Kofin Duniya
A ci gaba da gudanar da wasannin cin kofin kwallon kafa na duniya a kasar Rasha, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Senegal ta samu nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta Poland da ci 2 - 1 a wasanda suka gudanar dazu.
A wasan da kungiyoyin kwallon kafan na Senegal da Poland suka buga a yau, dan wasan Poland Thiago Cionek ne ya fara zura kwallo ta farko a ragar kasarsa a mintuna na 37 bisa kure.
Sai kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, dan wasan Senegal M'Baye Niang ya saka kwallo ta biyua mintuna na 60, amma a mintuna na 86 dan wasan Poland Grzegorz Krychowiak ya zura kwallo ta farko a ragar Senegal, kuma haka a ka ci gaba da wasan har aka kamma ba tare da Poland ta iya fanshewa ba.
Mai horar da 'yan wasan Senegal Aliou Cisse, ya bayyana wannan nasara da cewa ba ta Senegal ce ita kadai ba, nasara ce ta Afrika baki daya.