MDD : Yawan 'Yan Gudun Hijira A Duniya Ya Haura Miliyan 69
(last modified Wed, 20 Jun 2018 12:12:27 GMT )
Jun 20, 2018 12:12 UTC
  • MDD : Yawan 'Yan Gudun Hijira A Duniya Ya Haura Miliyan 69

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin DUniya ce ta sanar da adadin 'yan gudun hijirar da ake da su a duniya

Hukumar ta ci gaba da cewa adadin mutane miliyan 68 da dubu dari biyar na 'yan gudun hijirar yana a matsayin kaso daya ne da dukkanin mutanen duniya, kuma yake-yake da tashe-tashen hankula ne su ka ingiza su barin gidajensu.

Rahoton hukumar ya yi ishara da yadda ake da 'yan gudun hijira masu yawa a cikin kasashen Syria da kuma Myanmar.

Musgunawa al'ummar musulmin Rohinga da ake yi a kasar Myanmar ne sanadin ficewarsu daga cikin gidajensu da garuruwansu. A halin da ake ciki da akwai fiye da mutane miliyan guda da dubu dari biyu da su ke gudun hijira a kasar Bangaladesh.

A cikin kasashen Somaliya da Iraki da Sudan da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da akwai wani adadi mai yawa na 'yan gudun hijira