Majalisar Dinkin Duniya Ta Kara Wa'adin Zaman Dakarunta A Kasar DR Congo
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kara wa'adin zaman dakarun Majalisar Dinkin Duniya da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na tsawon shekara guda.
A zaman da ya gudanar a jiya Laraba: Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya dauki matakin kara wa'adin ci gaba da zaman dakarun Majalisar Dinkin Duniya da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na tsawon shekara guda tare da jaddada samun hadin kai tsakanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya {MONUSCO} da rundunar sojin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo musamman a fagen yaki da kungiyar 'yan tawayen Ruwanda ta Democratic Forces for the Liberation of Rwanda ta "FDLR" da kuma sauran kungiyoyin 'yan tawayen kasar, kamar yadda kwamitin tsaron ya yi tofin Allah tsine kan kisan kare dangi da aka yi wa al'ummar yankin Beni har 500 a cikin watan Oktoban shekara ta 2014 yana mai jaddada yin kira ga mahukuntan kasar ta Dimokaradiyyar Congo kan hanzarta bankado wadanda suke da hannu a wannan kisan kiyashi domin hukunta su.
Har ila yau kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada yin kira ga mahukuntan kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da su tabbatar da ganin an gudanar da zabuka cikin gaskiya da adalci tare da bai wa al'umma 'yanci zaben shugabannin da suke son su wakilce su gami da jaddada yin kira ga Hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta "CENI" kan ta shirya zabuka cikin adalci a duk fadin kasar.