Najeriya : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Raunana Mutun 15 A Borno
Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa, mutane akalla 15 sne suka raunana, yayin da wasu 'yan kunar bakin wake biyu mata suka tarwasa kansa a wata barikin soji dake jihar.
Harin dai na ranar Laraba ya haifar da hargitsi a barikin, kuma duka 'yan kunar bakin waken biyu sun hallaka a yayin hare haren da aka kai a wata mashaya dake cikin barikin sojin.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edet Okon, ya ce sojoji sun harbe 'yar kunar bakin wake ta farko, yayin da take kokarin sayen tikitin shiga babbar kasuwar dake cikin barikin, Ita kuwa 'yar kunar bakin wake ta biyu, ta tada abun fashewar ne a cikin wani mashin na a daidaita sahu.
Babu dai wata kungiyar data dau alhakin kai hare haren, saidai sau tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'adi ga kungiyar nan da aka fi sani da boko haram.