'Yan Adawa Na Hankoron Ganin An Safke Shugaba Zuma
Mar 31, 2016 10:33 UTC
Babbar jam'iyyar adawa a kasar Afirka ta kudu na hankoron ganin an safke shugaba Zuma saboda batun almubazzaranci.
Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta Afirka ta kudu ta sanar da hakan ne bayan da kotu ta tabbatar da zargin da ake yi wa shugaba Zuma na yin amfani da kudade ba ta hanyar da ta dace wajen gyaran gidansa.
Kotun dai ta baiwa shugaba Zuma kwanaki 45 domin ya mayr da kudaden domin , kuwa a cewar kotun abin da ya yi na amfani da kuadden gwamnati wajen gyara wuraren da ba su da alaka da tsaro ya sabawa doka.
An zargi Jacob Zuma da yin amfani da kudaden ne wajen gyara wuraren tarbar baki, da gidan dabbobi a gidansa na kashin kansa.
Tags