An Kashe Fararen Hula 32 A Tsakiyar Mali
(last modified Sun, 24 Jun 2018 15:53:08 GMT )
Jun 24, 2018 15:53 UTC
  • An Kashe Fararen Hula 32 A Tsakiyar Mali

Rahotanni daga Mali na cewa a kalla fararen hula fulani 32 ne suka rasa rayukansu a wani hari da ake danganta wa dana mafarauta da ake kira ''Dozo'' a yankin.

An dai kai harin ne a ranar Asabar data gabata a kauyen Kumaga dake yankin Djene a jihar Mopti dake tsakiyar kasar, kamar yadda babbar kungiyar Fulani ta Mali ta shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP.

Shugaban kungiyar Tabila Pullaku, Abel Aziz Diallo, ya kuma shaida cewa akwai wasu mutane goma da ba'a gansu ba.

Galibin mutanen da aka kai wa harin fararen hula ne ciki har da yara, a cewar wani kansila a yankin, wanda bai so a ambaci sunansa ba.

Babu dai karin bayyani daga hukumomin kasar ta Mali akan al'amarin a cwar labarin.

Yau kusan shekaru uku kenan da yankin tsakiyar Mali ke fuskantar rikici, na tsakanin Fulani makiyaya da kuma 'yan kabilar Bambara da kuma Dogon wadanda galibi manoma ne.