Russia 2018 : Senegal Ta Yi Kunnen Doki Da Japan 2-2
A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da Rasha ke karbar bakunci, an tashi kunnen doki tsakanin tawagar kwallon kafa ta Senegal da Japon 2-2 a wasaninsu na biyu biyu da suka buga da maraicen yau a rukunin H.
Senegal ce ta fara zuwa kwallo a ragar Japan a mintina 11 , kafin daga bisani Japan ta rama a mintina 34 da soma wasan, inda kuma aka je hutun rabin lokaci kasashen na 1-1.
Sai bayan dawowar hutun rabin lokaci kuma Senegal ta sake zura kwallo na biyu, a mintina na 71, inda nan ma Japan ta rama kwallon a mintina na 78 da dawowa wasan.
Kasashen biyu dai suk sunyi iyakacin kokarinsu saidai sun tashi kunnen doki.
A halin yanzu Senegal da Najeriya ne suka rage a cikin kasashen dake wakiltar nahiyar AFrika a gasar ta bana.
Nan gaba Senegal zata yi wasanta na uku da Columbia a ranar 28 ga watan nan a birnin Samara, a yayin da Najeriya zata yi wasan ta na uku a ranar Talata mai zuwa inda za ta fafata da Argentina.