Mali: An Cafke Wani Jagoran 'Yan Ta'adda
Mar 31, 2016 06:12 UTC
Jami'an tsaro na kundumbala na kasar Mali sun cafke wani babban jagora a cikin kuniyoyin 'yan ta'adda na kasar masu da'awar jihadi.
Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin bamako ya bayar da rahoton cewa, an cafke Sulaiman Kita jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta Khalid Bin Walid a kan iyakokin kasar ta Mali da Mauritaniya, kuma an dauke shia jiya Laraba zuwa birnin Bamako.
Sulain Kita dai babban na hannun damar Iyad Ag Gali ne jagoran kungiyar Ansaruddin, sun kasance tare tare a lokacin da suke yaki a arewacin Mali a cikin 2012, amma bayan kai hare-haren da Faransa ta yi, ya gudu ya koma kudancin kasar, inda ya kafa wata kungiyar 'yan ta'adda mai suna Kata'ib Khalid Bin Walid.
Tags