Mali: An Yi Wa Fararen Hula 50 Kisan Kiyashi
Jun 25, 2018 08:14 UTC
Wasu masu dauke da makamai da ba a tantance su ba, sun kai hari a kauyen Mopti da ke tsakiyar kasar Mali inda su ka kashe mutane 50
Kafafen watsa labarun kasar Mali sun ce wasu karin mutane 14 sun jikkata kuma wasu 10 sun bace.
Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan wadanda su ka kai harin, sai dai wasu rahotannin na nuni da cewa rikici ne na kabilanci.
Yankunan arewaci da tsakiyar kasar ta Mali na fuskantar rikici irin wannan wanda yake haddasa zubar da jini.
Tare da cewa da akwai dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na kasar Faransa a cikin kasar ta Mali, sai dai harkokin tsaro ba su inganta ba.
Tags