Russia 2018 : Hankalin Afrika Ya Koma Ga Senegal
(last modified Thu, 28 Jun 2018 05:34:06 GMT )
Jun 28, 2018 05:34 UTC
  • Russia 2018 : Hankalin Afrika Ya Koma Ga Senegal

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar Rasha ke karbar bakunci, a yanzu dai hankalin 'yan Afrika ya koma ga kasar Senegal, wacce zata buga wasansa na uku da Columbia a yau.

Senegal dai na bukatar ko yin kunnen doki da Columbia, don samun tsallakawa a wasanin gaba, a yayin da tuni sauren takwarorinta daga Afrika, Morocco, Masar, Tunisia da Najeriya aka yi waje dasu a gasar ta bana.

Mai hora da 'yan wasan na tawagar kwallon kafa ta Senegal, Aliou Cissé, ya bayyana wa manema labarai cewa, babu bata lokaci akan wani dogon, ''nasara kawai ake bukata''

A wasanin da aka buga a jiya dai, Koriya ta Kudu ta yi waje da kasar Jamus, mai rike da kofin duniya, bayan data doke da ci 2-0, sai kuma Switzerland da Cosra Rica da sukayi kunnen doki 2-2, a yayin da Brazil kuma ta lallasa Serbia ita ma da ci 2-0. 

Wasu wasannin da za'a buga yau Alhamis, sun hada da Japon - Poland, sai Ingila - Belgium, sannan Panama da Tunisia.